Hukumar Hisbah Ta Kano Na Kokarin Ganin An Ware Wajen Zaman Mata Da Maza Daban A Cikin Motocin Haya


Babban kwamandan hukumar Hisba ta jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa, yayi kira da a rika ware maza da mata a cikin ababen hawa domin bawa mata darajarsu da Allah ya basu.

Malam Daurawa ya bada wannan shawarar lokacin wani taron yini guda na wayar dakai da ofishin mai bawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje, shawara kan babura masu kafa uku, Abdullahi Shitu ya shirya.

Shugaban ya  gabatar da mukala kan matsayin addinin musulunci game da dangantaka tsakanin mace da namiji a cikin abin hawa musamman mai kafa uku wanda akafi sani da Adaidaita Sahu.

Ya ce ” Mata suna da matukar kima, musulunci  ya girmama su, duk wanda ya girmama mace to ya girmama mahaifiyarsa, shi yasa Allah bai bar kowa yazo duniya ba face ta jikin mace, musulunci ya koyar, ya kuma yi umarni tare da wa’azi kan girmama mata hakan ya haɗa da kare su da kuma kula da su. Saboda haka kuskure ne mace ta zauna kusa da mutumin da mijinta ba har takai suna gugar kafada.

Ya shawarci masu hayar babura masu kafa uku da suyi amfani da sana’arsu wajen bautawa Allah da kyautatawa mutane kana su kaucewa aikata duk wani abin da bai dace ba, shaye-shaye  da kuma dabi’un da suka saba wa musulunci da za su iya shafar addininsu.

You may also like