Hukumar Hisba ta jihar Kano ta kama mabarata 55 cikin watan Satumba kan zarginsu da karyar dokar da ta hana yin bara akan tituna dake fadin jihar.
Wani ma’aikaci a hukumar dake ɓangaren dake kula da yaki da bara, Dahiru Muhammad, yace 17 daga cikin wadanda aka kama kananan yara ne yayin da 38 suka kasance manya.
A cewar sa 33 daga cikin su sun fito ne daga jihar Kano,22 daga jihohin Abia, Bauchi, Katsina da kuma jihar Jigawa.
Muhammad yace an gudanar da kamen ne a bakin bata,kan titin France,da kuma titin Katsina dukkansu a cikin birnin Kano.
Ya ce hukumar ta saki mabaratan da wannan karon aka fara kama su da kuma wadanda suke fama da tabin hankali yayin da wadanda suka fito daga makotan jihohi aka mayar dasu kananan hukumomin su.