Hukumar kiyaye Haddura TaSa Wa’adi Na Haramta Wa Direbobin Tanka Tafiyar DareHukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta sanya ranar 19 ga watan Disamba a matsayin Wa’adi na karshe na Haramtawa Direbobin tanka mai yin tafiyar dare a duk fadin Nijeriya inda ta dauki alwashin hukunta duk wani direba da ya karya dokar.
Da yake karin haske kan dokar, Shugaban Hukumar na Kasa, Corps Marshal Bobaye Oyeyemi ya nuna cewa matakin ya zama dole don tsaftace harkar jigilar mai tare da rage yawan hadarin tankokin mai a kan titunan kasar nan. Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda hadurran tankokin mai kan janyo asarar rayuka da dukiyoyin mutanen da basuji ba kuma basu gani ba

You may also like