Hukumar Kula Da Yanayi Ta Najeriya Ta Yi Hasashen Cewa Za A Kara Samun Ambaliyar Ruwan Sama A BanaABUJA, NIGERIA – NiMET ta yi hasashen sake aukuwar iftila’in ambaliyar ruwan sama a Jihohin da aka fuskanci hakan bara, wannan dai na kunshe ne cikin kundin bayanan hasashen yanayi na shekarar 2023 da aka fitar wanda ya yi nuni da cewa a bana ruwan sama zai sauko da wuri a wasu wurare da ke sassan Najeriya sabanin yadda aka saba gani a baya.

A cewar NiMET, ruwan sama zai sauka da wuri a cikin watan Maris a yankunan Kudu maso Kudu masu iyaka da teku wadanda suka hada da Jihohin Bayelsa, Rivers da Akwa Ibom, sai kuma wasu daga cikin Jihohin yankin Arewa da suka hada da Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Kano, Katsina, Jigawa, Gombe da kuma Borno daga watan Yuni zuwa watan Yuli.

Hukumar Kula Da Yanayi Ta Najeriya Ta Yi Hasashen Kara Samun Ambaliyar Ruwan Sama A Bana

Hukumar Kula Da Yanayi Ta Najeriya Ta Yi Hasashen Kara Samun Ambaliyar Ruwan Sama A Bana

A baya dai gwamnati da masu ruwa da tsaki sun sha daukar matakan kare al’umma don takaita aukuwar iftila’in dake zuwa da sauyin yanayi.

Haka kuma, ministan sufurin jiragen sama ta Najeriya Sanata Hadi Sirika, ya ce shekarar 2022 ta zama manuniya ga kasar kuma babban darasi sakamokon irin tsananin asarar rayuka da dukiyoyi da ambaliyar ruwa ta haifar a wasu yankuna na sassan kasar, yana mai cewa a adalilin hakan ya sa aka fidda kundin bayanan hasashen yanayi na bana akan lokaci don ya zama manuniya kan hanyoyin da suka dace a shirya tunkarar duk wani yanayi da ka iya zuwa a bana mussamam ga wasu bangarorin dake da matukar muhimmaci ga tattalin arzikin kasa.

Hukumar Kula Da Yanayi Ta Najeriya Ta Yi Hasashen Kara Samun Ambaliyar Ruwan Sama A Bana

Hukumar Kula Da Yanayi Ta Najeriya Ta Yi Hasashen Kara Samun Ambaliyar Ruwan Sama A Bana

Wasu kasashe da ke da makwabtaka da Najeriya kamar Jamhuriyyar Nijar da Gambiya sun bayyana aniyarsu ta amfani da hasashen da hukumar NiMET ta fitar don tunkarar duk wani cikas da ka iya zuwa da sauyin yanayi a bana.

An dai bukaci al’umma da su yi amfani da bayanan kundin hasashen sauyin yanayi na hukumar NiMET wanda aka fassara cikin manya harsunar kasar wajen daukan matakai da suka dace da wuri da kuma rage radadin asarar da ake samu sakamokon matsanancin yanayi a Najeriya.

Saurari cikakken rahoto daga Shamsiyya Hamaza IBrahim:Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like