
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafar Faransa ta aike da sakon wasika ga rafli da cewar kada su tsayar da wasa domin masu azumi su buda baki a lokacin tamaula.
Ranar Juma’a aka ci gaba da wasannin Ligue 1, inda Marseille ta tashi 1-1 da Montpellier, bayan kammala wasannin kasa da kasa da Fifa kan ware ranakun.
Kamar yadda Mailonline ta wallafa, ta ce an samu sakon da hukumar ta aikewa alkalen tamaula a fadin kasar da cewar za ta dakatar da duk wanda ya tsayar da wasa domin shan ruwa ko buda baki a gefen fili lokacin da ake tamaula.
Musulmai na yin azumi a watan Ramadan tun daga farko har karshensa, inda aka bukaci kauracewa ci da sha tun daga asuba zuwa faduwar rana.
Wannan umarnin daga hukumar kwallon kafar Faransa ya ci karo da na mahukuntan Premier League da suka umarci alkalan wasa su bayar da takaitaccen hutu, domin ‘yan wasan da ke dauke da azumi su yi buda baki a gefen fili.
Premier ta umarci masu azumi su sha ruwa da cin abinci mara nauyi don buda baki a gefen fili na wani takaitaccen lokaci, sannan a ci gaba da taka leda.
Ita kuwa Chelsea ta bayar da izini da magoya baya su je Stamford Bridge, domin buda baki tun daga ranar da aka fara azumin shekarar nan.
Tuni hukumar kwallon kafar Faransa ta ja kunnen alkalan tamaula a kasar da kada su tsayar da wasa don buda baki, saboda haka duk dan kwallon da ke dauke da azumi, sai an kammala tamaula zai buda baki.