
Asalin hoton, OTHER
Hukumar kwallon kafar Faransa ta kai karar golan Argentina Emiliano Martinez, saboda salon murnar da ya yi a wasansu na karshe na gasar kofin duniya.
Martinez ya taka rawa sosai a wasan musamman a bugun fenareti da suka yi nasara.
To amma wasu hotuna sun nuna shi rike da diyar roba mai siffar dan wasan gaban Faransa, Kylian Mbappe, a lokacin da suke murnar lashe kofi a birnin Buenos Aires.
Wasu rahotanni sun ce har neman a yi shiru na minti daya ya yi ga Mbappe a dakin saka kaya bayan kammala wasan.
Hakan yasa Shugaban hukumar kwallon kafar Faransa, Noel Le Graet ya rubuta takarda ga takwaransa Claudio Tapia, ta neman su hukunta golan bisa dabi’ar da ya nuna.
Shima kocin Aston Villa da Martinez ke buga wasa, Unai Emery ya ce zai tattauna da golan kan salon murnar da ya yi idan ya dawo hutu daga Argentina.
A ranar 26 ne za a dawo fagen daga a gasar Premier League ta Ingila.