Hukumar Kwastan A Nijar Ta cafke Wasu Dururrukan Man Fetur Da Akayi Fasa Kwaurin Su Daga Najeriya


Jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasar Nijar tare da hadin gwiwar ‘yan sanda sun cafke duro duro da jarkokin Man Fetur, wadanda ‘yan fasa kwauri suka boye a wani kauye a birnin Yamai.
Masu masa kwauri dai sun ketarar da Man Fetur din ne ta hanyar amfani da kwale kwale daga Najeriya, hakan yasa jami’an kwastam sukayi kira ga ‘yan kasar da su basu hadin kai domin yaki da wannan harmatacciyar sana’a.
Jami’an kwastam sun sami nasarar kame duro duro har 341 hade da jarkoki 76 shake da Man Fetur a wani sumame da suka gudanar a kauyen Abdagungu dake da nisan Kilomita 15 daga birnin Yamai. Masu fasa kwarin dai suna boye Man Fetur dinne a gidaje da dama, bayan sunyi amfani da jiragen kwale kwale sun ketaro da Man daga Najeriya.
Damuwa da irin barazanar da ajiyar Man Fetur ke yiwa rayuwar jama’ar kauyen ne yasa suka tseguntawa hukumomi abin da ke faruwa. Kamar yadda kanal Ahya Alhaji ya fada lokacin da aka gabatarwa da manema labarai wadannan kayayyaki.
Baya ga haka hukumar kwastam tace ta sami nasarar kama wata motar tanka mai lambar jihar Kebbin Najeriya, dauke da lita Dubu 40 na Man Fetur lokacin da ta ketaro daga Najeriya da takardun bogi.
Masu fasa kwaurin dai sun sami gamin bakin wasu mutanen kauyen cikinsu har da hakimin garin kansa inji kanal Mohammadu Harzuka shugaban rundunar yaki da ‘yan fasa kwauri, wanda kuma yace “baya ga koma bayan da yake haddasawa tattalin arzikin kasa fasa kwarin Man fetur wani abu ne dake barazana ga rayuwar jama’a da ta muhalli.”
A watannin baya dai wasu dinbin mutane sun rasa rayukansu a gundumar Matamaye dake jihar Zindar a sanadiyar gobarar da ta tashi bayan da wata mota shake da Man fasa kwauri ta kama da wuta, lokacin da direbanta yake kokarin tserewa jami’an kwastam.

You may also like