Hukumar Kwastan Ta Fara Binciken Takardar Harajin Shigo Da Motoci (Custom Duty) A yau Litinin ne hukumar hana fasakwabri ta Nijeriya (Nigerian Custom) za ta fara tantace takardun haraji na shigo da motaci (Custom Duty), domin gane mai kyau da marar kyau, wadanda basu biya ba kuma su biya kafin wa’adin da ta bada na fitowa sarari domin bincike kan mai uwa da wabi.
In baku manta ba, a wannan watan ne shugaban hukumar kanar Hamid Ali ya saka hannu a wata takarda mai dauke da cewa, daga ranar 12  ga watan 4, hukumar zata bibiyi dukkan wata mota ta sayarwa ko ta hawa wadda batada takardan haraji na shigowa (Custom Duty), zata kame wadannan motoci har sai sun biya wadannan kudaden kamar yadda doka ta tanada.
Tuni dai Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaban hukumar Kanar Hamid Ali ya baiyana a gaban majalisar ranar laraba don ba da bahasi kan matakin da hukumar ta dauka na lalle za ta kwace duk tsoffin motocin da ba a biya musu kudin harajin ba.
Majalisar dai na adawa da wannan manufa da nuna hakan zai takurawa talakawa, Kazalika majalisar ta bukaci Kanar Ali ya baiyana gaban ta sanye da kayan sarki na kwastam da ba a taba gani ya sanya ba tun nada shi mukamin a 2015.
Hamid Ali dai ya ce zuwa yanzu bai ma samu takardar gaiyata daga majalisar ba, kuma sam ba zai sanya kayan sarki na kwastam ba, Ali yace ba kaya ya dace majalisar ta duba ba, amma aiki ya dace ta yi la’akari da a na gudanar da shi bisa ka’ida ne ko kuwa a’a.
Ku a ganinku, kamata ya yi a ja layi, ma’ana a kyale wadanda suka shigo, a maida hankali ga wadanda za su shigo anan gaba ko a’a?

You may also like