Hukumar Kwastan Ta Kona Tulin Kaji Da Ta Kama A BeninHukumar Kwastan ta kasa ta bayyana cewa ta kona kwalaye 16,422 makare da danyen Kaji wanda aka kiyasta kudinsu a kan Naira Milyan 147 bayan ta kama kayayyakin a Kogin Ovia da jihar Benin.
Shugaban Hukumar na shiyyar, Usman Shehu Dabiru ne ya bayyana haka inda ya nuna cewa an kama kajin ne a cikin wata Babbar mota mai lamba BDG 654 XL da misalin Karfe takwas na dare. Ya ce hukumar ta bi matakin kona kajin ne bisa umarnin gwamnatin tarayya na haramta shigowa da Kaji daga waje.

You may also like