Hukumar Kwastan Ta Koro Manyan Jami’anta Guda 29


Hukumar kwastan ta sallami manyan jami’anta 29 bayan ta same su da aika manyan laifuka.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a yau Alhamis ta ce, mutanen na cikin jami’anta 44 da ta hukunta saboda aikata wasu laifuka da ke barazana ga sha’anin tsaro da kuma tattalin arzikin kasar.
A makon jiya ne, hukumar ta kori jami’anta guda 17 saboda samun su da laifukan da ke da nasaba da karbar cin hanci da ta’ammuli da miyagun kwayoyi da kuma amfani da takardun shaidan karatu na jabu har ma da rashin halartar wurin aiki.
Tun bayan nadin Kanar Hamid Ali mai ritaya a matsayin shugaban hukumar, ya bayyana cewa, hukumar ba za ta amince da cin hanci da rashawa da kuma munanan dabi’u tsakanin jami’anta ba.

You may also like