Hukumar SEMA ta musanta samun asarar rai a Kaduna sakamakon motsawar kasa


 

 

Hukumar bada agajin gaggawa SEMA da ke jihar Kaduna a Najeriya, ta ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon motsawar da kasa ta yi a kauyen Kwoi a karamar Hukumar Jaba a Kudancin jihar.

Sakataren Hukumar ta SEMA Ezekiel Baba-Karik ya kuma musanta rahotannin da ke cewa, an kuma samun motsawar kasar a Kauyukan Nok da Sambang Dagi, da ke karamar hukumar ta Jaba kamar yadda wasu ke yadawa.

Baba-Karik ya ce tuni aka aike da tawagar masu bincike yankin domin gano musabbabin motsawar kasar.

You may also like