Hukumar Shirya Jarabawar UTME Ta Soke Sakamakon Dalibai 59,698


Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB, ta tabbatar da soke sakamakon jarabawar UTME ta  dalibai 59,698 kan zargin aikata magudin jarrabawa. 

Ishaq Oloyede, magatakardan hukumar ya bayyana haka ranar Laraba a Abuja, yayin wani taron manema labarai bayan kammala taron masu ruwa da tsaki a harkar gudanar da jarrabawar ta UTME.

A cewarsa an soke sakamakon mutane 1,386 kan samun su da aikata magudin jarrabawa, mutane 57,646 su kuma an soke sakamakon nasu bayan da aka samu cibiyoyin da suka zana jarrabawar da taimakon  aikata magudin, yayin da aka soke sakamakon mutane 666 sakamakon samunsu da yin jarrabawar fiye da daya. 
Sakamakon da aka soke yayi kasa da adadin sakamakon jarrabawar da hukumar ta rike bata saka ba.

Akwai yiyuwar za a sake baiwa wasu daliban damar sake rubuta jarrabawar musamman ma wadanda aka samu cibiyar da suka zana jarrabawar da laifi, tunda dai basu su suka aikata laifin ba.  

You may also like