Tsohon ministan abuja sanata Bala Mohammed da dansa sun rasa gidaje hudu(4)wanda kudin su zai kai naira milliaan dari takwas da sabain da biyu(N872) a hanun kungiyar yaki da cin hanci da rashawa(EFCC).
Bala yayi aiki karkashin mulkin sugaban kasa Goodluck Jonatan kuma bincike yanuna cewa ana tuhumarsa da cin kudin contarakin naira billiaan daya.
hukumar tace ana cigaba da binciken shi akan bada manyan filaye guda takwas wadanda kudaden su kai bilyoyin kudi da kuma wasu filaye guda talatin da bawai (37)dukansu za su kai kimamin naira billiaan takwas(N8) ga wani Tariq Hammoud. kuma ana bincike akan kudin kasa naira trillian daya(N1).fiye da kamfanoni goma sha sida aka zarga da karbar kwangila a wajen sanatan kuma a yanzu haka hukumar tana gudanar da bincike a kan kamfanoni.
hukumar ta tsare Shamsudeen hammoud da manyan darectocin Abuja har da na daractan adana kudi,Ibrahim Bomoi;da na filaye Babayo mainasara da kuma Jamila Tangaza.