Hukumar ‘yan sanda a Zimbabwe ta haramta zanga-zanga tsawon wata guda


 

zimbabwe-demos

 

Hukumar ‘yan sandan kasar Zimbabwe, ta bayyana dakatar da gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Harare, har tsawon wata daya.

Shugaban rundunar ‘yan sanda na birnin Harare Newbert Saunyama, ya ce dokar zata fara aiki daga ranar 16 ga watan Satumba, zuwa ranar 15 ga watan October.

A baya wata babbar kotu a kasar, ta soke dokar haramta zanga-zanga na tsawon sati biyu, da hukumar ‘yan sandan kasar ta kafa, inda kotun ta ce ba’abi ka’ida ba wajen kafa dokar, zalika dokar ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Zimbabwe na fama da koma bayan tattalin arziki wanda ya sa yanzu haka a kasar rashin aikin yi ya zarta kashi 80% cikin 100%, abinda yasa wasu daga cikin mutanen kasar fusata da gwamnatin Shugaba Robert Mugabe.

 

You may also like