Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Ta Gargadi ‘ Yan Shi’a Da Kada Su Gudanar Da Kowanne Irin Zanga-Zanga A jiharKakakin ‘yan sandar jihar Kaduna Aliyu Usman ya fadi hakan ne a wata takarda da hukumar ta fitar a yau.
Aliyu Usman ya kara jaddada wa jama’a cewa kungiyar tsaron da aka fi sani da (Civilian JTF) ba ta da amincewar gwamnati kuma ya gargade su akan yin wani abinda zai jawo rashin zaman lafiya a jihar.

Bayan haka Hukumar ta ce duk kungiyar da ta yi zanga-zanga ba tare da izini ba, za ta hukunta ta daidai da yanda doka ta shimfida.
Kuma ta shawarci kowa da ya cigaba da gudanar da harkokinsa sannan kowa ya kula kuma a kai karan duk abin da aka gani na shakku da ba a yarda da shi ba musamman a wannan lokaci na karshen shekara.

You may also like