Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta shirya tsaf domin fara cigaba da yiwa masu kaɗa ƙuri’a rijista a dukkanin ƙananan hukumomi 774 dake faɗin ƙasar nan.
Daraktan yaɗa labarai da kuma ilimantar da masu kaɗa kuri’a Oluwole Osaze Uzzi,ya bayyana haka jiya Laraba a Abuja.
Ya faɗawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN cewa an tura dukkanin kayayyakin da ake buƙata domin fara aikin kamar yadda aka tsara.
“An tura ma’aikata da kuma kayan aikin da ake buƙata, mun kuma bawa ma’aikatan mu horo, waɗanda zasu kasance ofisoshin hukumar dake ƙananan hukumomi”yace
“Duk kanin kwamishinoninmu sun tafi shiyoyinsu don ƙaddamar da fara aikin, yayin da shugaban hukumar zai ƙaddamar da shirin a Abuja.”
Osaze yace za’a gudanar da shirin a ofisoshin hukumar ta INEC dake ƙananan hukumomi, a ranakun aiki, tun daga ƙarfe 9 na safe har zuwa 3 na yamma.
Darakatan ya shawarci waɗanda suka rasa katin zaɓensu dama waɗanda ba suyi rijistar ba da suyi amfani da wannan dama.
Ya kuma ƙara da cewa babban laifine mutum yayi rijistar fiye da ɗaya.