Hukumar Zabe Ta Yi Watsi Da Bukatar Jam’iyyar PDP Na Daga Zaben Jahar Ondo


 

Hukumar zabe a Nijeriya ba ta amince da bukatar Jam’iyyar PDP na a dage zaben Gwamnan Jahar Ondo ba, wanda za’a yi a karshen wannan mako.

Hukumar ta bayyana dalilinta da cewa Jam’iyyu guda ne 28 suka tsayar da ‘Yan takara a zaben, saboda haka ba za ta dage zaben ba saboda bukatar Jam’iyyar PDP

Jam’iyar ta PDP ta bukaci dage zaben ne saboda ta samu damar warware rikicin da ke cikinta inda ‘yan takara har biyu ke ikirarin tsayawa takarar.

Jam’iyyar na son a bata lokaci don bai wa kotun koli damar yanke hukunci kan takaddamar da ke tsakanin ‘yan takarar biyu; Eyitayo Jegede da Jimoh Ibrahim.

Sai dai hukumar ta kafe akan yin zaben a ranar da aka tsaida, wato Lahadi, 26 ga wannan watan na Nuwamba.

You may also like