Hukumar Zakka Ta Jihar Kano Ta Yi Wa Marayu Gata


Hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano ta raba zakka ga daruruwan jama’a wadanda suka hada da marayu da sauran mabukata da suka cancanci samun zakka a makon da ya gabata.

Kwamishina na daya a hukumar, Barista Habibu Dan Almajiri ne ya bayyana haka a ofishinsa, lokacin da Majalisar Mahaddata Alkur’ani ta Kasa, reshen Jihar Kano karkashin jagorancin Goni Sunusi Abubakar ta ziyarce hukumar.

Da yake gabatar da Jawabi lokacin da yake karbar tawagar mahaddatan, Barista Habibu Dan Almajiri ya bayyana farin cikinsa da ziyarar inda ya tabbatar wa da Alarammomin cewar za a ci gaba da gudanar da duk abubuwan da suka taso tare da majalisar tasu musamman wajen samar da gudunmawar da duk ta kamata.

Kwamishinan ya bayyana irin kokarin da wannan hukuma ta yi musamman a watan azumin da ya gabata, inda aka raba kudade da abubuwan bukata ga daruruwan marayu da masu bukata, baya ga raba zakka ga matan dake kula da marayun da kuma wadanda mazajensu suka mutu suka bar masu yara, sai kuma zawarawa da ke bukatar tallafi domin samun saukin rayuwa.

A jawabinsa, Shugaban Mahaddata na Jihar Kano, Goni Sunusi Abubakar wanda har ila yau shi ne Sakataren Kwamitin Amintattu na Mahaddata na Kasa, ya yaba da zakakuran mutanen da aka damka wa alhakin gudanar da harkokin Hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar.

Ya bukaci hukumar ta shigar da Mahaddata cikin ayyukanta na alhairi musamman idan aka yi la’akari da bukatun da Almajirai da Alarammomi ke da su ta fuskar zamantakewa. Jagoran Mahaddatan ya tabbatar wa da kwamishinan cewa wannan majalisar a shirye take wajen taimaka wa duk wani shiri da zai kawo wa wannan gwamnati ci gaban da ake bukata.

Wakazalika, Babban Daraktan Hukumar Zakka da Hubusin ta Jihar Kano, Goni Safiyanu Ibrahim Gwagwarwa ya tabbatar wa da majalisar mahaddatan cewa za a ci gaba da tallafa wa wannan majalisa, inda ya bukace ta ta rubuto abubuwan da suke fatan ganin hukumar ta shigo ciki domin tallafawa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like