Hukumomin Binciken Kudi Na Tarayya Sun Gano Kimanin Naira Bilyan 450 Da ba’a Sakasu A Asusun Gwamnati ba



A jiya Alhamis ne ministar kudi Misis Kemi Adeousun a wani taron manema labarai tace, an yi bincike a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin tarayya daban-daban don gano ko suna aiki da umarnin sabon tsarin ajiyar kudi na bai daya, wato TSA.
Binciken wanda babban akanta na kasa ya jagoranta, ya gano kusan rarar naira bilyan 450 daga ma’aikatu da hukumomi daban-dabam, wanda ba a dawo da su asusun ba, daga shekarar 2010 zuwa 2015.
A cewar ministar, wasu ma’aikatun sun fara dawo da wasu kudaden, ciki har da hukumar da ke kula da jiragen ruwa ta kasa NSC, da ta dawo da Naira miliyan 640.

You may also like