Ya kuma bayyana dalilin da ya sa ba a yi masa hukunci a laifi makamancin haka ba
Fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan, Ali Nuhu, ya ce hukuncin da kungiyar masu hada finafinan Hausa, MOPPAN ta yi na korar Rahama Sadau, ya yi tsanani.
Ya ce kamata ya yi a dauki hukuncin da bai kai na kora ba kamar dakatar da ‘yar wasan na dan wani lokaci.
Sai dai kuma Ali Nuhu wanda ya shaida hakan a wata hira da jaridar Daily Trust, ya ce ‘yar wasan ta karya dokokin kungiyar.
Dangane kuma da mutanen da suka rinka yayata hotunan jarumin rungume da mata, a kafafen sada zumunta, Ali Nuhu ya ce, ya yi hotunan ne da dadewa tun kafin kungiyar MOPPAN ta haramta yin hakan.
A makon da ya gabata ne dai kungiyar ta MOPPAN ta sanar da korar Rahma Sadau daga harkar finafinan Hausa saboda rungumar wani mawaki.