
Asalin hoton, Google
Manufar azumi shi ne kame baki da farji don samun yardar Allah mahalicci.
Shi ne ya ce babu wanda zai iya biyan ladan azumi sai shi da kansa.
To amma ya shimfiɗa sharuɗɗa waɗanda rashin kiyaye su, na iya ɓata azumi gaba ɗaya, ko kuma a gurgunta sahihancinsa.
A ɓangaren kame baki, ba kawai an hana mai azumi ƙauracewa abinci da abin sha ba ne, kalamai marasa ma’ana da rashin yi wa baki linzami na iya jefa ibadar mutum cikin garari.
Gulma da annamimanci da cin naman mutum, duk abubuwa ne masu matuƙar illa ga azumi.
Albarkacin watan Ramadan mai alfarma, BBC ta tattauna da Malama Maijidda Aliyu Harazimi a kan hukuncin gulma a wajen mai azumi.
Malama Maijidda ta ce Ubangiji ya bayyana cewa “ya sanya azumi ya zama watan da saukar Ƙur’ani a ciki,… har zuwa yadda yake cewa ko za ku kasance cikin nutsattsu”, wannan yana nuna yadda ake son mutum ya zama na kirki cikin wannan wata mai alfarma.
Gulma a karan kanta, ba ta karya azumi, amma tana kassara shi, haka ma sauran ibadun da ake yi a cikin wannan wata.
“Idan ya kasance an haramta ta (gulma) a wajen azumi, to ina ga lokacin azumin shi kansa? ka ga ai abu ne wanda Ubangiji ba ya so”. in ji Malama MaiJidda.
Mece ce gulma
Gulma a cikin addini ta sha banban da abin da ake kira ƙazafi.
“Annabi Muhammad ya tambayi sahabbansa cewa me suka fahimta da gulma? sai suka ce ka yi maganar mutum kan wani abu da ya yi a bayan idonsa wanda idan ya ji hakan, ba zai ji daɗi ba.
“Gulma ba ta da haddi a addini, amma kuma tana ɓata aiki,” in ji Malama.
Ta ce ƙazafi ya fi muni domin shi magana ce a kan mutum, kuma kan abin da bai yi ba, kuma yana da haddi a cikin addini daidai da girmansa.
“Yana cikin abubuwa bakwai da Annabi ya ce mutane su guje su, don kuwa masu hallakarwa ne”.
A cewarta, don ba ka jin shakkar faɗar magana maras kyau a bayan idon mutum wadda, kana da yaƙinin za ka iya maimaita ta a kan idonsa, kada ka yi tsammanin ba gulma kuka yi ba. Ita ce ma, cikakkiyar gulma!