Idan Ba A Magance Talauci ba,  Abinda Zai Biyo Baya Yafi Rikicin BokoHaram – Kashim Shettima 



Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya ce idan ba’a magance matsaloli kamar na matsanancin talauci da ake fama dashi ba da kuma bunkasa harkar ilimi ba ga marasa galihu, to abinda zai biyo bayan rikicin Boko Haram, zai yi muni idan ba’a maida hankalin kan wadannan batutuwa ba.
Kashim Shattima, ya furta haka a lokacin da kwamitin sa ido kan yadda aka kashe kudaden da aka kebewa ‘yan gudun hijira, karkashin jagorancin sanata Shehu Sani, suka ziyarce shi a gidan Gwamnati.

You may also like