Idan Ba Ai Hankali Ba Nigeriya Zata shiga cikin Matsanancin Rashin Abinci – Gwamnatin Tarayya 


Idan Ba A Yi Kaffa-kaffa Ba Nan Da Kankanin Lokaci Za A Yi Matsanancin Rashin Abinci A Nijeriya, Cewar Fadar Gwamnatin Tarayya
Mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya sanarwa da gidan rediyon Pyramid dake jihar Kano cewa idan ba a yi kaffa-kaffa ba, za a sami matsanancin rashin abinci musamman wadanda suka shafi hatsi a Nijeriya zuwa watan Janairu.
Garba Shehu ya fadi hakan ne ganin yadda kasashen dake makwabtaka da Nijeriya suke shigowa suna siye abincin da aka girbe.
Yace kasashe kamar su Algeriya, Libya, har Brazil sun shigo suna ta siye hatsi da manoma suka girbe musamman a Kano, Kebbi, Jigawa da Katsina.
Ya ce akalla tireloli 500 ne duk mako suke fita da abinci daga Nijeriya.. 

You may also like