Mun samu labari daga Jaridar The Nation cewa tsohon Ministan Neja-Delta a lokacin Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi kaca-kaca da Jam’iyyar PDP a wata takarda da ya aika inda yace yanzu Jam’iyyar ta kama layin bata.
Tsohon Ministan Neja-Delta yace Jam’iyyar PDP na cikin matsala
Godwin Elder Orubebe yayi kira ga Jam’iyyar PDP da su yi maza su kama shirin gyara idan ba haka ba kuwa Jam’iyyar za ta shiga cikin littatafan tarihi.
Orubebe yace har yanzu Jam’iyyar PDP ba ta cikin hayyacin ta tun zaben 2015.
Tsohon Ministan ya koka a wata wasika da ya rubutawa Shugaban Jam’iyyar da yadda kama-karya da kuma girman kan wasu ya sa Jam’iyyar ta sha kashi a 2015 musamman a wajen taron gangamin da ta shirya na karshe a lokacin.
Mista Orubebe yace dole PDP ta yarda cewa tayi kuskure lokacin da tayi mulki. A cewar tsohon Ministan, gajiyawar Jam’iyyar ta sa Obasanjo ke kokarin kafa wata Kungiya.
Orubebe ya kuma nemi PDP ta nemi kudi gudun kar wasu daidaiku su saye Jam’iyyar.