Gwamna Ayo Fayose na jihar Ekiti ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kira shi a waya domin ya tabbatarwa ‘yan Najeriya gaskiyar lamari akan lafiyarsa.
A cewar sa, ” Na shawarci shugaban kasa ya yi magana da ni domin gamsar da ‘yan Najeriya ya na nan Garau, maimakon ya rika kiran wasu don a yarda kalau ya ke.”