Ilimin ‘ya’ya Mata arziki ne


2016-10-19t155041z_831837231_s1beuhwxvtaa_rtrmadp_3_nigeria-bokoharam

 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce gwamnatocin da suka inganta kula da lafiyar yara mata da kuma ba su nagartaccen ilimi na iya bunkasa tattalin arzikinsu sama da Dala biliyan 21. Sannan rahoton ya ce ilimi ga yara mata zai yaki talauci a kasashe masu tasowa.

Rahotan Hukumar kula da yawan jama’a ta Majalisar UNPFA ya bayyana cewar yara mata a kasashe masu tasowa ba su samun damar kammala karatu kamar takwarorinsu maza, saboda yadda ake tilasta mu su aure da wuri da saka su aikin karfi da matsalar kaciya da kuma Karin wasu matsaloli.

Rahotan ya ce yara mata 47,700 ake yi wa aure ‘yan kasa da shekaru 18 a duniya kowacce rana.

Sannan rahoton ya ce yawanci Yara mata ba su samun damar ci gaba da karatu a Sakandare a kasashen Larabawa da Afrika, wadanda ke da yawan Mata ‘yan kasa da shekaru 10.

Wani rahoton shekara da kungiyar kare hakkin yara kanana ta Save the Children ta fitar a bana ya ce an bar yara mata a baya saboda matsaloli na rashin daidaito da karfafawa.

Kungiyar ta ce Dan Adam ba zai samu nasara da cikkaken ci gaba ba idan aka hanawa wani bangare na rabin al’umma samun ‘yancinsu a matsayinsu na  ‘Yan Adam.

Save The Children ta zayyana matsaloli uku da ta ce suke tauye ci gaban mata da suka hada da Aure da wuri da rashin samun abubuwan more rayuwa da karfin fada aji ga harakoki na yau da kullum.

Rahoton kungiyar ya ce cikin dakika bakwai ana aurar da Yarinya ‘yar kasa da shekaru 15, sannan duk shekara ana aurar da Yara mata miliyan 15 ‘yan kasa da shekaru 18.

You may also like