Illar Shaye-Shaye: Wani Matashi Ya Cakawa Kansa WukaWani Matashi mai suna Umar Mande, mai kimanin shekaru 35, ya cakawa kansa wuka a garin Potiskum ta jihar Yobe. Amma cikin ikon Allah bai mutu ba. 

Yadda al’amarin ya faru kuwa shine, shi dai wannan matashi, shi da abokanansa suna shaye shayen su a wata Mashaya da ake kira Dorawa a cikin garin Potiskum, sai rikici ya hada su akan Giyar Wiski, wadda takai ga har shi Umar Mande ransa ya baci, saboda ba a bashi ya sha ba. 

To wannan bacin ran ne yasa ya cakawa kansa wuka a cikin sa, inda nan take ya fadi, aka dauko shi cikin gaggawa zuwa babban Asibitin Potiskum. Yanzu haka dai Likitoci suna kokarin ceto rayuwarsa a babban Asibitin Potiskum, sannan kuma Jami’an tsaron ‘yan Sanda, suna binciken lamarin.

You may also like