Illar Shaye-Shaye: Ya Kone Kansa Sabida Takaicin Lalata Da Mahaifiyarsa Cikin MayeBabban Malami Ibn Uthaimeen a Sharhinsa ga littafin Bulugul Maram, babin haramcin giya, yace ya taba karantawa a wata majalla cewa wani matashi ya sha giya yazo ya samu mahaifiyar shi cewar yana so ya sadu da ita, ita kuma ta nuna mashi ba zata yarda ba.

Kawai sai ya dauko wuka yace indai bata yarda ba to zai kashe kanshi, sai tausayi ya kamata, sai ta kyale shi ya sadu da ita. Da gari ya waye hankalinshi ya dawo mashi, sai ya tambayi mahaifiyarshi me ya faru jiya da dare, tace mashi ba komai. Ya matsa mata ta fada mashi, sai ta fada mashi, kawai sai hankalinshi ya tashi yaje ya zuba ma jikinshi fetur ya kona kanshi. 

Shaye-Shaye yana da illa sosai, shi ke jawo miji ya kashe matarshi ko mata ta kashe mijinta.

You may also like