Illoli bakwai da kwana da garwashi a lokacin sanyi ke haifarwa



.

Asalin hoton, Qoura

A yayin da ake ƙara shiga sanyi, masana a fannin lafiya a Najeriya sun gargaɗi alumma da su kauce wa kwana da garwashin wuta saboda illolin da yake da shi ga lafiya.

Masanan dai sun ce kwana da garwashin wutar kan haifar da wasu cututtuka da ke shafar numfashi, da illa ga fatar jikin dan Adam.

Gargaɗin likitocin na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka samu wasu ma’aurata da ake zargin sun rasa ransu sakamakon kwana da irin wannan garwashi a daki yankin Ƙarmar hukumar Dawakin Tofa a Kano.

A irin wannan lokaci na sanyi, akan saka garwashin a ɗaki domin ya yi ɗumi. Sai dai kwararru na cewa hada wuta sasakai a daki yana da matukar hadari.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like