
Asalin hoton, Google
Watan Ramadana wata ne mai alfarma da ba a bai wa wasu al’umma ta baya ba irinsa, sai al’umar Annabi Muhammad.
Cikin watan akan ruɓanya ayyukan alkhairi zuwa wani adadi da Allah ne kawai ya bar wa kansa sani.
Ko wanne minti ɗaya cikinsa lokaci ne mai matuƙar tsada da ba a sake samun irinsa sai wata shekarar ga wanda aka bai wa tsawon rai.
Malamai da dama na yawan jan hankali wajen ganin mutane sun rabauci wannan dama da Ubangiji ke ba su.
Amma a mafi yawan lokuta sai ka ga wasu sun mayar da hankali kan kafafen sada zumunta maimakon ruɓanya ayyukan alkhairi kamar yadda addinin Musulunci ya nema.
A wannan karon, BBC ta yi nazari kan yadda mutane ke ɓata lokaci a waɗannan kafafe, kuma take tambaya kan cewa ko hakan yana da illa?
Malam Muntasir Umar Mai Fenta muka tattauna da shi, kuma ya ce ba ƙaramar asara ɗayanmu ke yi ba na ƙarar da lokutansa a kafafen sada zumunta.
“A dukkan kafafen sada zumuntar da muke da su babu wanda kake da ikon abin da zaka gani a cikinsa, kama daga TikTok da Facebook da Instagram har ma da WhatsApp, zaka iya karo da bidiyo ko hoton da ba ka shirya gani ba, da zai iya zama illa ga lafiyar azuminka,” in ji Malam Muntasir.
Abu ne sananne ga duk masu hawa kafafen sada zumunta, bidiyo ko hoton tsaraici zai iya fado maka kwatsam, wanda haramun ne ganin hakan a waje da cikin azumi, kamar yadda malam ya ƙara da cewa.
Mafi munin abubuwan nan shi ne TikTok, ka je kana kallon tsaraicin mata, ko muharramarka ba a son ka kalli tsaraicinta balle wadda ba ka sani ba, kwata-kwata nisantar kafafen sada zumuntar ya fi alfani.
A cewar Malam, Ƙur’ani ya yi bayani a bayyane cewa “Ganinka da saurarenka duka abubuwa ne da za a tambaye ka a kansu”.
Abin da aka fi so mutum ya shagalta da su sune: karatun ƙur’ani zikiri da istigfari, kwana 30 ko 29 ne kacal, yanzu za su ƙare.
In baka amfana da watan ba, ka yi abubuwan ibada, la’alla ka ƙare da samun zunubi mai yawa na kallon abubuwan da ba su dace ba.
Bayan nan, abin da muke wallafawa shi kansa akwai ayar tambaya a kansa, saboda da yawanmu mun iya cin mutunci ko izgilanci ko kalaman da za su tunzura mutane, wani lokacin ƙarya ma muke wallafawa.
Duka waɗannan abubuwa saɓo ne, dole mutum ya kiyaye.