Imam Imam mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal mutu.
Imam ya rasu da karfe uku na daren Juma’a a asibitin Nizamieye na yan kasar Turkiyya dake Abuja.
Abubakar Imam wani kaninsa shine ya tabbatar da mutuwarsa.
Za dai ayi jana’izarsa a masallacin Annur dake Abuja da misalin karfe 1:30 na rana bayan an kammala sallar Juma’a.
Yan uwa , abokanan aiki da kuma masu bibiyar kafafen yada labarai na cigaba da bayyana alhininsu na rasuwarsa a kafafen sadarwar zamani.
Marigayi dan asalin jihar Taraba ne ya rasu ya bar mata biyu da kuma ‘ya’ya hudu.