In An Jima Ne Shugaban Kasar Amurka Na 45 Donal Trump Zai Yi Rantsuwar Kama Aiki A Matsayin Shugaban Kasa


A dai dai lokacinda magoya da kuma masu adawa da zabebben shugaban kasar Amurka Donal Trump shirye shiryen karbar mulki suna tafiya kamar yadda aka tsara.

Jaridar washington post ta bayyana cewa an fara shirye shiryen karban mulki a birnin washington tun jiya Alhamis bayan isowar zabebben shugaban kasar daga jihar ta NewYork tare da iyalansa da kuma na kusa da shi.

A yau jumma’a ne sabon shugaban zai yi rantsawar kama aiki, a dai dai lokacinda masu adawa da kuma goyon bayansu suke jefe jefe a tsakaninsu a wasu wurare a birnin na washinton.

Wasu yan adawa suna kwatanta Trump a matsayin mai nuna wariyar da kuma bambancin a cikn Amurkawa, da wannan dadlilin ne ma suke cewa bai cancaci shugabancin kasar ba.

Maganganu da kuma jawaban da Trumps ya yi tayi kafin da bayan an zabe shi ya sanya mutanen da kuma manya manyan kasashen Turai suke sukansa kan rashin iya bakinsa da kuma dagula lamura a duniya da ma cikin kasar kafin ya fara aiki.

You may also like