INA BAKIN CIKIN SIYASAR KUDI DA KASHE-KASHE  – BUHARI Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa yana bakin ciki kan yadda ‘yan siyasa ke amfani da kudi da kuma fitina don kawai su cimma wata buri ta siyasa.

Buhari ya bayyana haka ne a Kano bayan ya kammala ziyarar kwanaki biyu inda ya bayar da misali kan abubuwan da suka faru a zabukan da aka yi a jihohin Kogi, Bayelsa da kuma Rivers inda mutane da dama suka rasa rayukansu bayan kuma yadda aka yi amfani da makudan kudade wajen jan ra’ayin jama’a.

You may also like