
[the_ad id=”3197″]
Daya daga cikin wadanda rundunar sojin Najeriya ta wallafa sunasu a jaridu cewar ana neman su ruwa a jallo Aisba Wakili tace; Gaskiya ne ina da alaka da BokoHaram kuma kunsan hakan ba tun yanzu ba.
Ta kara da cewa, sanin kanku ne cewa ina da alaka da ‘yan Boko Haram tun kafin lokacin da suka sace’ yan matan Chibok. Domin ina daya daga cikim ‘yan kwamitin sulhu tsakanin gwamnati da’ yan Kungiyar.
Nayi iya bakin kokari na wajen bawa gwamnatin Najeriya shawara tare dayi musu alkawarin kawo musu shugabannin kungiyar ta BokoHaram domin gano bakin zaren da kuma sakin ‘yan matan da aka kama, amma basu saurare niba sunci gaba da yin al’ amuran su iya su kadai.
Nayi mutukar mamaki danaga sunana acikin wadanda ake nema, babban abin mamakin shine harda sunan mijina aka hada wanda hakan ba karamin tashin hankali bane da iyalai na baki daya.