Ina Gargadin El’Rufa’i Daya Kiyaye ni – Sen Shehu SaniTun bayan munmunan hari da muggan makamai da wasu matasa wadanda ake kyautata zaton cewa magoya bayan gwamnan jihar Kaduna Nasiru El Rufa’i ne suka kai akan ofishin yakin neman zabe na Sanata Shehu Sani a Kaduna, inda suka jikkata ma’aikata dake gudanar da ayyukansu a cikin ofishin, jama’ar jihar ke ta faman bayyana ra’ayoyinsu akai.
A wani taron manema labarai da Kwamared Shehu Sani ya kira a gidanshi dake Kaduna, ya gargadi El Rufa’i da cewar hawainiyarshi ta kiyayi ramarshi, domin muddin gwamnan ya ce zai cigaba da takalarshi ko shakka babu zai gane kurenshi domin yana jin labarin Shehu Sani ne amma bai san wanene kwamared ba.
Sanata Shehu Sani ya cigaba da cewar, baya kasa Nijeriya lokacin da ‘yan bangan El Rufa’i suka kai hari ofishinshi dauke da muggan makamai Bindigogi Barandami da sauransu, sannan suka kaddamar da sara akan magoya bayanshi dake gudanar da aikace aikacensu a ofishin, lamarin da yayi sanadiyar jikkata da dama daga cikinsu.
Dan Majalisar dattawa ya kuma bayyana wannan hari da magoya bayan El Rufa’i suka kaiwa magoya bayanshi a matsayin wani al’amari daya kara sanya mishi karsashi ya kuma karfafeshi da cigaba da yakar mulkin danniya da ake gudanarwa a adin jihar.
Sanata Shehu Sani ya kara da cewar idan ana magana APC a jihar Kaduna toshi jigo ne a cikinta domin da hannunshi dumu dumu wajen kafa jam’iyyar a jihar, da kuma shugabannin jam’iyyar, sabanin El Rufa’i wanda ya fado cikin jam’iyyar da rana tsaka, bayan anci an cinye PDP dashi, saboda haka babu yadda za’ayi dan cirani ya kori dan gari daga cikin jam’iyya.
Kwamared Shehu Sani wanda ya nuna damurwashi da yadda El Rufa’i keta faman kashe kudaden jihar kaduna wajen yaki dashi, inda ya bayyana cewar wadannan kudade da gwamnan ke kashewa wajen yada farfaganda ta karya a kanshi, da kudin da akace ana biyan Fulani makiyaya dashi domin su daina kai hare hare a kudancin jihar kaduna, kamata yayi gwamnan yayi amfani dasu wajen inganta rayuwar jama’ar jihar wadanda suka fita hayyacinsu saboda talauci.
A nasu bangaren jam’iyyar APC magoya bayan Nasiru El Rufa’i su shelanta korar Sanata Shehu Sani daga cikin jam’iyyar, biyo bayan abinda suka kira taurin kai da rashin girmama shugabannin jam’iyyar da Sanatan yakeyi.
Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar APC a jihar Malam Salisu Wusuno ya bayyana hakan, a wani taron manema labarai da jam’iyya APC ta kira a ofishinta dake titin Ali Akilu a garin kaduna.
Salisu Wusono ya kara da cewar da kyar sukasha daga hannun gungun wasu matasa magoya bayan Sanata Shehu Sani, wadanda suka kawo musu hari a Ofishin nasu dauke da manyan makamai.
Saidai a yayin da manema labarai suka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rudunar ‘yan sandan jihar kaduna ASP Aliyu Muhammed ya karyata magoya bayan gwamnan, inda yace babu wani hari da aka kai a ofishin APC na jihar Kaduna.
Garin Kaduna dai na cigaba da shiga cikin rudani da zullumi tsakanin jama’ar garin sakamakon wannan rikici wanda yaki ci yaki cinyewa tsakanin shugabannin biyu wadanda suka fito daga jam’iyya guda.

You may also like