Ina Godia Ga ‘Yan Najeriya Baki Daya Bisa Addu’o’in Su Da Nuna Damuwa Gareni – Buhari



A karon farko tun ranar 31 ga watan Janairu, a daren jiya Laraba, shugaba Muhammadu Buhari ya rubuta sako a shafin sa na Twitter inda ya ke godewa ‘yan Nijeriya, musulmi da Kirista game da addu’o’in da suke masa na samun lafiya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin majalisa suka ziyarci Buhari a masaukinsa dake birnin London a yammacin jiya.
A sakon da shugaban ya wallafa, ya kuma godewa shugabbin majalisa Bukola Saraki, Yakubu Dogara da Ahmed Lawan da kai masa ziyara.
Shugaba Buhari dai ya na birnin London inda ya ke hutu da kuma duba lafiyar sa tun ranar 19 ga watan Janairu.

You may also like