Ina JaJantawa Al’ummar Kasata kan Halin da suke Ciki –  Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa al’ummar kasar kan halin kuncin da suka samu kan su wanda yace na lokaci ne kadan, ganin irin matsalolin da suka addabi kasar.
Yayin da yake jawabin cika shekaru 56 da samun yancin kai, Buhari ya ce ya san abinda ke zuciyar duk wani dan kasar yau shine matsalar tattalin arziki da kuma kuncin rayuwa.
Yace a matsayin sa na wanda ya dogara da albashi iya rayuwar sa, kuma wanda ya san cewar albashin yau bai iya kai ma’aikaci ko ina, yana yabawa al’ummar kasar kan irin dauriyar da suke nunawa.
Shugaban ya bukaci yan kasar kada su rufe idan su kan matsalolin da ake fuskanta wadanda yace na wucin gadi ne domin gwamnati ta dauko gyara dan ganin komai ya inganta.
Buhari ya bayyana damuwar sa kan yadda tsagerun Niger Delta ke ci gaba da fasa bututun mai har ma da wanda ke tura mai kasashen waje wanda ya kai ga kasar bata iya fitar da ganga sama da miliyan guda daga ganga sama da miliyan biyu da ta saba yi kowacce rana.
Bayan ya baiwa al’ummar kasar hakuri kan halin da suka samu kan su, shugaban ya kuma bayyana ayyukan gina hanyoyi da dama da samar da wutar lantarki da gina gidaje da akeyi a fadin kasar.

You may also like