Ina kokari matuka wajen samarwa da matasa aikin yi – Buhari


Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya ce gwamnatinsa tana kokari matuka wajen ganin ta samarwa da matasa aikin yi.

Da yake magana a fadar shugaban kasa a ranar Talata lokacin da yake karbar bakuncin, Boukekri Rmilli  ministan harkokin wajen kasar Tunisia, Buhari ya ce gwamnatinsa na zuba jari mai yawa a fannin noma.

Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya rawaito shugaban kasar na alkwarin cewa gwamnatinsa za ta kara tallafin da take bayarwa a fannin noma a matsayin wata hanya ta samar da aiyukan yi.

“Bayan rashin tabbas a kasuwar mai da kuma tarin matsalar rashin aikin yi a kasarnan mun dora makomar mu akan harkar noma.Ina farin ciki matasan mu na rungumar harkar noma maimakon su jira aiki a ofisoshi.”Buhari ya ce.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta ga cigaban  da kasar Tunisia ta samu a fannin Noma, yawon bude ido da kuma kiwon lafiya kuma nan bada jimawa ba zai tura wata tawaga ta kai ziyara kasar domin gano bangarorin da kasashe biyun za su iya yin aiki tare da juna.

Rmilli wanda ya jagoranci wasu tawagar yan kasuwa ya shedawa shugaban kasar cewa kasarsa ta kagu ta kara habaka alakar kasuwanci da Najeriya.

You may also like