Ina matsayin ibadar mai azumin da ba ya sallah?



Sallah

  • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
  • Twitter,

Addinin Musulunci ya wajabta sallah kan duk Musulmi baligi kuma mai hankali a halin zaman gida ko na tafiya da yaƙi a kan namiji da mace – sai dai akwai uzuri a kan mace mai jinin al’ada da na biƙi.

Sallah ibada ce mai girma wadda ta kasance rukuni na biyu cikin rukunan Musulunci.

Ita ce ta raba tsakanin mutum da shirka da kafirci, kuma ginshiƙi ce ta rayuwar ibadar Musulmi.

Yayin da aka shiga azumin watan Ramadan mai alfarma, Musulmai kan ninka ko su ƙara riƙo da ibadunsu na farilla kamar sallah da sauran ayyukansu na alheri.





Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like