Ina Matukar Jin Kunyar Nuna Ni Attajiri Ne- Dangote


Hakika bani da wani gida a wajen Najeriya. Ina sauka a hotel cikin sauki. Rayuwata ba mai tsada ce ba, sannan hakika ina matukar jin kunya in na nuna ina da arziki. Don haka bana yi. Ina yawaita shawartar mutane akan ya fi a koda yaushe ka zamo mai matukar shiga mutane.

A Legas, ina tuka kaina a cikin karshen sati. Ina cewa mai tukina yaje ya huta, sannan sai in tuka kaina inda nake so. Har yanzu Ina ziyartar abokaina, domin na tashi da hakan.

Gidana a bude yake a koda yaushe garesu. Ina yin mu’amala da kowa. Ta haka ne kawai zaka san abin da yake faruwa.

You may also like