Ina so na yi aure amma… – Hadiza Gabon


 

 

Shaharariyar ‘yar fim din Kannywood din nan, Hadiza Gabon, ta ce tana so ta yi aure amma lokaci ne kawai bai yi ba.

Da take hira da BBC, Hadiza ta ce aure lokaci ne, kuma kamar mutuwa, idan Allah ya kawo shi babu yadda mutum zai guje masa.

“Wallahi babu wata mace da za ta so ta kai lokacin aure amma ta ki yi” inji Gabon.

Jarumar, wacce ta lashe kyautar ‘yar wasan da ta fi tallafawa babban jarumi a fim ta Africa Films Awards na bana, ta ce tana kaunar duk masu goyon bayanta.

Hadiza Gabon, ta ce babu wacce za ta so ta rinka kaiwa-tana-komowa a gaban iyayenta ba tare da ta yi aure ba, alhalin kuma ta kai munzalin yin hakan.

A hirar da Ahmed Abba Abdullahi ya yi da ita da kuma Ali Nuhu, jarumar ta yi kira ga masu kaunarta da su yi mata addu’a.

Ahmed Abba Abdullahi tare da bakin BBC Hausa, Ali Nuhu da Hadiza Gabon
Image captionAli Nuhu da Hadiza Gabon sun ziyarci sashin Hausa na BBC

Ta kara da cewa duk wata ‘yar fim “da ka gani, to wallahi tana so ta yi aure”.

Muna so mu yi, amma babu yadda muka iya saboda ba za mu auri kanmu ba.

“A don haka addu’a muke nema daga wurinku,” a cewarta.

Ana sa bangaren Ali Nuhu ya yaba yadda jarumar ta koyi harshen Hausa da Turanci, da kuma irin rawar da take takawa a fim.

You may also like