
Asalin hoton, OTHER
Dan wasan gaban Najeriya Victor Osimhen ya ce yana jin dadin zamansa a kungiyarsa Napoli.
Ya ce ba shi da niyyar barin kungiyar a watan Janairu, don yana da burin cin kofin Serie A na Italiya da kungiyar ta birnin Naples.
”Tana daya daga cikin manyan kungiyoyin Turai kuma ina son cin kofi a nan,” inji Osimhen”, in ji Osimhen.
Napoli na bugun lokacinta bana a Serie A, inda ta ci wasanni 13 ta yi kunnen doki biyu, kuma har yanzu ba bu wanda ya doke ta.
Yanzu haka ta hada maki 41, kuma ta bai wa AC Milan da ke binta maki takwas a teburin na Serie A.
Rabon da Napoli ta lashe kofin Scudetto na Serie A tun 1990, lokacin marigayi Diego Maradona.
Kungiyoyi da dama na son daukar Victor Osimhen, wanda ya ci wa Napoli kwallaye 10 a kakar bana.