Mai mata 90 da ‘ya’ya sama da dari, Malam Muhammadu Bello Masaba wanda yake da zama a garin Bidda dake jihar Niger, ya musanta jita-jitar da aka yi ta yadawa na cewa ya rasu, inda a hirarsa da majiyarmu ya bayyana cewa yana nan cikin koshin lafiya.
A shekarun baya dai Malam Bello Masaba ya yi ta shan tsangwama daga wurin jama’ar gari da Malaman addini saboda auren mata da yawa da ya yi wanda ake ganin ya sabawa addinin musulunci duk yana ikrarin cewa shi malami ne.