Ina Rubuta Littafi Kan Yadda Muka Kayar Da Jonathan A Zaɓen Shekarar 2015 – Tinubu


Tinubu

Jagoran jam’iyar APC Bola Ahmad Tinubu yace yana rubuta littafi akan yadda jam’iyarsa ta APC ta samu nasarar raba shugaban ƙasa mai mulki da muƙaminsa a zaben 2015.

An yabawa Tinubu kan rawar da ya taka na kawar da jam’iyar PDP dake mulkin gwamnatin tarayya a zaɓen shekarar 2015.

Tinubu na wannan jawabi ne a wurin bikin ƙaddamar da littafin da shahararren marubucin nan kuma ɗan jarida  Olusegun Adeniyi, ya rubuta mai suna “Against the Run of Play” a bikin da ya gudana a birinin Lagos.

Tinubu yace nan ba daɗewa ba zai faɗi labarin yadda ya kafa APC, domin ta kawo ƙarshen mulkin jam’iyar PDP na tsawon shekaru 16. Tinubu wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa  kan harkokin kafafen yaɗa labarai, Tunde Rahman.

“Wasu sunce zasu faɗi nasu labarin, Asiwaju  shima yana aiki kan nasa littafin domin faɗin abainda yafaru”

“Yafaɗi yadda ya haɗa kan jam’iyar APC har takai yadda ta iya kawar da shugaban ƙasa  mai mulki daga kujerarsa a karon farko a tarihin siyasar Najeriya”

Ya kuma ce, rasa kujerar mataimakin shugaban ƙasa da yayi baza a iya haɗashi ba, da nasarar da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo yayi ba.

Tinubu ya ƙara da cewa yayi zaɓe mai da ya zaɓi Osinbajo a matsayin wanda zai yi wa shugaba Buhari mataimaki.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like