Indiya : Mutane 24 Suka Mutu A Wani Tumutsutsu Wajen Ibada


 

 

‘Yan sanda a Indiya sun ce mutane 24 na suka mutu a yayin wani turmutsutsu wayen ibada a arewacin kasar.

19 daga cikin wadanda suka mutu a turmutsutsun mata ne, kana akwai wasu akallah mutane 20 da suka raunana a cewar sanarwar.

Lamarin dai ya auku a lardin Varanasi dake yankin Uttar Pradesh, a lokacin da masu ibada ke bi kan wata gada dake kaiwa zuwa wurin haduwar.

Babban sfeto ‘yan sanda yankin ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa lamarin ya auku ne sanadin yawan mutane dake kan tsohuwar gadar ta karfe.

Turmutsutsun a cewarsa ya auku bayan samun rade raden cewa gadar na kan ruftawa inda mutane sukayi ta gudu.

You may also like