Indonesia zata karrama wanda ya kamo fitinannen Kada


146394776_0

 

 

Gwanmatin kasar Indonesia ta tsaida shawarar biyan wasu makudan kudade ga duk wanda da ya kawo mata kada, da ransa cikin wadanda suke hana sakat a gabar teku dake gabashin kasar.

 

 

A alkawarinta duk wanda ya cimma nasarar wannan farauta zai kwashi garabasar amshe kudi daya kai dalar Amurka 380, kwatankwacin kudin kasar samada Rupiah miliyan 5.

Wadannan kadoji dai yanzu haka sun hana sakat a gabar tekun gabashin kasar, inda suke hana baki masu yawon shakatawa zuwa.

Ba’a kashe kada, karkashin Dokokin kasar ta Indonesia.

You may also like