INEC ta kori jami’anta biyu kan laifin yi wa Yahaya Bello rijistar zaɓe sau biyu


Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta kori wasu ma’aikatanta biyu da ake zarginsu da hannu wajen yiwa gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello rijistar yin zaɓe har sau biyu.

Hukumar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun May Agbamuche-Mbu daya daga cikin kwamishinonin hukumar na kasa.

Bello wanda yayi rijistar zabe a matsayin mai kada kuri’a  a birnin tarayya Abuja an ce ya sake yin rijista a Kogi a lokacin da aka fara ci-gaba da yiwa masu zabe rijista a cikin watan Mayu.

 Yin rijista sau biyu ya saba da doka.

INEC ta kafa kwamiti domin  ya binciki abinda ya faru.

Sai dai Bello ya musalta zargin da ake masa na aikata ba dai-dai ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like