INEC Ta kudiri Aniyyar Dakike Yawan Amfani Da Kudi A Lokacin Zabe A Najeriya
Shugaban hukumar zabe ta Najeriya INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a yayin taron masu ruwa da tsaki kan duba tasiri da illar fitar da makudan kudade da ‘yan siyasa a kasar ke yi, tare da kari kan cewa ba za’a lamuncewa duk wani dan siyasa da ke barazana sayen imanin al’umma da kudi ba a babban zaben kasar dake tafe, don haka hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da sayen kuri’un zabe a kasar.

“Muna da kwamiti wanda ya hada jamia’an tsaro na kasa baki daya da wasu ma’aikatu da suke da ruwa da tsaki game da harkar kudi a zabe, saboda haka zamu sake zama dasu domin sake duba me zamu sake yi nan gaba” A cewar wani dan siyasa.

Kazalika hukumar watsa labarai ta NBC a Najeriya ta ja kunnen duk kafofin yada labarai kan su yi taka tsantsan wajen yada manufar ‘yan takarkaru ko jam’iyyu da kuma karban kudi daga garesu la’akari da cewa tsarin zaɓe na zuwa da kashe kuɗi mai yawa, don haka su ajiye shaida kan duk wata hada-hada da ta kasance a tsakani.

“Kafafen yada labarai basu bari an yi amfani da su ba wajen yin kazamin kudi ta tallace tallace ko kuma wasu abubuwa makamnacin haka ba……” a cewar shugaban hukumar Malam Balarabe Shehu Ilelah.

A na shi bangaren shugaban kungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa a Najeriya, Injiniya Yabagyi Sani ya kalubanci jami’an tsaro da su yi aiki bisa jajircewa da kuma kishin kasa domin yin hakan zai samar da tsabtaccen zabe da ake fatan samu a kasar.

“To idan lallai jami’an tsaro sun jajirce sun tashi sun yi aiki ma al’ummar Najeriya ba aiki wa gwamnati mai ci yanzu ba to lallai kam za’a samu wani canji….”in ji Injiniya Yabagyi Sani.

Itama Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta bayyana cewa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an samu nasara a matakan da aka dauka na dakile hanyoyin sayen kuri’u dama yawan kashe-kashen kudade da ‘yan siyasa ke yi a wannan lokaci na gangamin yakin neman zabe, ta hanyar sanya ido a rumfunan zabe, bincike, da gurfanar da duk wanda aka kama da laifi yin hakan a cewar Hajiya Hadiza Gamawa Zubairu shugaban ma’aikata na hukumar.

Masu ruwa da tsakin dai sun yi kira ga jam’iyyun siyasa da su bi ka’idojin zabe da kuma bayyana cikakkun hanyoyin samun kudaden yakin neman zabensu na shekarar 2023.

Saurari cikakkan rahoto daga Shamsiyya Hamza Ibrahim.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like