INEC ta sa ranar ƙarasa zaɓukan da ba a kammala baFarfesa Mahmud Yakubu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta sanya Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar ƙarasa zaɓukan da ba su kammala ba a jihohi da dama na ƙasar.

A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin, INEC ta ce ta yanke wannan shawara ce bayan wata ganawa tsakanin manyan jami’anta.

Akwai zaɓukan gwamnoni kamar a jihohin Kebbi da Adamawa, waɗanda jami’an sanar da sakamakon zaɓe suka ce ba su kammala ba a ranar 18 ga watan Maris, baya ga sauran zaɓukan ‘yan majalisun dokoki, da su ma suka fuskanci irin wannan cikas.

Ɗaya daga cikin jihohi da aka samu zaɓukan da ba su kammala ba masu yawa a ranar 25 ga watan Fabrairu, ita ce Sokoto, inda ake da ‘yan majalisar wakilai 11 da sanatoci 3 waɗanda duk zaɓensu bai kammalu ba.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like