Hukumar Zabe ta Ƙasa Mai Zaman Kanta INEC ta tsayar da ranar Asabar 1 ga watan Faburairu domin gudanar da zaɓen cike gurbi a wasu cibiyoyin zaɓe dake ƙananan hukumomin Mashi /Dutsi
Kwamishinan zaɓen jihar, Alhaji Jibril Zarewa wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai inda ya ce zaɓen cike gurbin zai gudana a cibiyoyin zaɓe 15 kamar yadda kotun ɗaukaka kararrakin zaɓe dake Kaduna ta umarta.
Ya ce cibiyoyin zaɓe 9 suna ƙaramar hukumar Mashi ya yin da 6 suke Dutsi inda ya ƙara da cewa ma’aikatan wucin gadi 150 da suka haɗa da masu bautar ƙasa za a yi amfani dasu wajen gudanar da zaɓen.
Ya nemi hadin kan dukkanin masu ruwa da tsaki a zaɓen domin samun nasarar zaɓen.
Idan za a iya tunawa ɗan takarar jam’iyyar PDP Nazifi Bello shine ya kalubalanci nasarar da ɗan takarar jam’iyar APC Mansur Ali ya samu a gaban kotun sauraran kararrakin zaɓen.